Kotu ta bawa EFCC umarnin ci gaba da tsare Bobrisky
Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Legas a Najeriya, ta sanar da ranar 9 ga watan Afrilun 2024 a matsayin ranar da za ta ci gaba da sauraron karar da take yiwa fitacen dan daudun nan Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky.
Wallafawa ranar:
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Bobrisky gaban kotun, kwana guda bayan bayyanarsa gaban hukumar ‘yan sanda da ke Legas, bisa zarginsa da wulakanta kudin kasar wato naira.
Mai shari’a Abimbola Awogboro, ya ayyana ranar ci gaba da sauraron karar ne, bayan da Bbrisky ya amsa laifuka hudu da ake tuhumarsa da aikatawa.
Kotun ta kuma bayar da umarnin cewa, Bobrisky zai ci gaba da zama a hannun hukumar EFCC har zuwa lokacin da za a yanke masa hukunci.
Hukumar yaki da masu yiwa arzikin Najeriya zagon kasa wato EFCC, ta gurfanar da Bobrisky gaban kuliya ne, bisa zarginsa da aikata laifuka shida, ciki kuwa har da batun wulakanta kudin kasar da kuma zargin almundahanar kudade.
Idan har kotun ta yanke masa hukunci bisa laifukan da ake zarginsa da aikatawa, Bobrisky zai yi zaman gidan yari har tsawon watanni shida ko kuma ya biya tarar naira 50,000, ko kuma ma kotun na iya hada masa wadannan hukunci baki daya a lokaci guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu