Isa ga babban shafi

An kone wasu gidaje a yankin da aka yi wa sojoji 16 kisan gilla a Delta

Gidaje da dama ne aka kona a kauyen Okuama da ke karamar hukumar Bomadi ta jahar Delta, bayan da aka kashe sojoji 16 da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Yadda wasu gidaje ke ci da wuta a garin Okuama na jahar Delta.
Yadda wasu gidaje ke ci da wuta a garin Okuama na jahar Delta. © channels
Talla

Wasu na zargin cewar, wasu fusatattun sojoji ne suka kori mutanen garin, bayan da aka kashe abokan aikinsu tare da gano gawarwakinsu a cikinsa.

Mutanen garin dai sun tsere zuwa Ughell da ke makwaftaka da su, saboda tsoron harin ramuwar gayya daga wajen sojojin da ke sintiri a garin.

Kawo yanzu dai ana ci gaba da farautar wadanda suka aikata laifin, inda ma rundunar sojojin Najeriya ta 6 karkashin jagorancin Manjo Janar Jamal Abdussalam, ta kama wasu da ake zargi kamar yadda babban hafasan tsaron Jahar Christopher Gwabin Musa ya bada umarni.

Gwamnan jahar ta Delta Sheriff Oborevwori, ya yi Allah wadai da faruwar lamarin, tare shan alwashin gano wadanda ke da hannu wajen aikita laifin.

Rahotanni sun nuna cewar lamarin ya faru ne a ranar Alhamis din da ta gabata, bayan da aka yi wa sojojin kiran gaggawa don su kawo dauki kan rikicin da aka samu tsakanin kauyukan Okuoma da kuma Okoloba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.