Isa ga babban shafi

Makarantun jihohin Najeriya 14 na fuskantar hatsarin harin ta'addanci - Gwamnati

Gwamnatin Najeriya ta fitar da jerin jihohin kasar 14 da makarantun su ke cikin hadari, dai-dai lokacin da ‘yan bindiga ke ci gaba da kutsawa makarantu suna garkuwa da dalibai.

Najeriya na fama da matsalolin masu garkuwa da mutane, lamarin da ke karuwa kusan kowacce rana
Najeriya na fama da matsalolin masu garkuwa da mutane, lamarin da ke karuwa kusan kowacce rana © AP/Matias Delacroix
Talla

Shugabar hukumar kulawa da makarantu ta kasar Hajiya Halima Iliya ce ta bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai, tana mai cewa jihohin sun hadar da Adamawa, Bauchi, Borno, Benue, Yobe, Katsina, birnin tarayya Abuja, Kebbi, Sokoto, Plateau, Zamfara da karin wasu guda 3.

Bayanin hukumar na zuwa ne kasa da mako guda bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da yara kusan 300 a jihar Kaduna, cikin su guda 28 sun tsere.

Kwana guda bayan nan kuma ‘yan bindigar suka sace daliban tsangaya 15 a jihar Sokoto

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.