Isa ga babban shafi

Kungiyar AANI ta yi wa gwamnatin Najeriya tayin bada shawarwari kan tsaro

Kungiyar Tsoffin Daliban Cibiyar Koyon Dabaru da Sha’anin Mulki ta Najeriya (AANI) ta yi Allah-wadai da ta’azzarar matsalar garkuwa da mutane tare da kasha-kashen da ‘yan ta’adda ke yi a sassan kasar.

Kungiyar Tsoffin Daliban Cibiyar Koyon Dabaru da Sha’anin Mulki ta Najeriya ta yi Allah-wadai da ta’azzarar matsalar garkuwa da mutane tare da kasha-kashen da ‘yan ta’adda ke yi a sassan kasar.
Kungiyar Tsoffin Daliban Cibiyar Koyon Dabaru da Sha’anin Mulki ta Najeriya ta yi Allah-wadai da ta’azzarar matsalar garkuwa da mutane tare da kasha-kashen da ‘yan ta’adda ke yi a sassan kasar. © NIPS-KURU
Talla

Kungiyar ta bayyana haka ne cikin wani jawabi da ta fitar dauke da sa hannun shugabanta Ambasada EO Okafor a jiya Asabar, inda ta ce ayyukan ta’addanci ‘yan bindiga a ‘yan kwanakin nan sun kara tabbatar da bukatar daukan matakin gaggawa domin kawo karshen wannan matsala.

Yayin da take yaba wa da kokarin da hukumomin tsaro ke yi kan abubuwan da ke faruwa, ta yi kira da a kara daukan sabbin dabarun zamani domin kawo karshen ta’addanci a kasar.

AANI ta kuma bayyana cewa a shirye take ta yi aiki da gwamnatin kasar wurin bada shawarwarin bunkasa dabaru tare da aiwatar da matakan tsaro a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.