Isa ga babban shafi

Tinubu ya kaddamar da layin dogo na 'Red line' a jihar Legas

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da wani sabon tsarin sifurin jiragen kasa na ‘Red line’ a jihar Lagos, wanda a kullum za’a dinga jigilar akalla fasinjoji kusan dubu dari biyar (500,000), a tsakanin Agege da Oshodi da Ikeja da Mushin da Yaba zuwa Oyingbo.

Hoton jirgin kasan Red Line da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kaddamar a Lagos
Hoton jirgin kasan Red Line da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kaddamar a Lagos © Lagos State Government/RFI
Talla

Layin dogon na 'Red line' ya tashi ne daga Marina ya bi ta unguwannin Yaba da Mushin da Oshodi da Agege, ya dangana har zuwa Ibadan, sannan ya bi har zuwa filin Jirgin Murtala Muhammad.

Da yake jawabi yayin kaddamar da tsarin sifurin na Red line, shugaba Tinubu ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na inganta abubuwan more rayuwa a kasar.

Shugaban kasar ya ce har yanzu yana kan bakaansa dangane da sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kudiri aniyar aiwatarwa.

Idan ba’a manta ba watan Satumbar shekarar 2023 ne tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da layin dogo na 'Blue line' a jihar wanda ya tashi daga Marina zuwa unguwannin Alaba da Mile 2 da Festac da Alajika da jami'ar LASU ya dangana zuwa Maintenance Deport.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.