Isa ga babban shafi

Gwamnatin Borno ta saki mutane 500 da aka tsare saboda zargin aikata ta'adddanci

Gwamnatin jihar Borno a Najeriya ta ce ta wanke wasu mutane  dari 5 da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci, kuma har ta bukaci a fitar da su daga inda ake tsare da su a barikin sojoji na Giwa da ke Maidguri.

Wasu mutanen da ake zargi da ayyukan ta'adanci da aka tsare a barikin Giwa na Maiduguri.
Wasu mutanen da ake zargi da ayyukan ta'adanci da aka tsare a barikin Giwa na Maiduguri. AP - Jossy Ola
Talla

Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar, Zuwaira Gambo ce ta bayyana haka a yayin da ta ke mayar da martani ga wasu mata da suka yi korafi a game da ci gaba da tsare maza da ‘yayansu, wadanda suka ce ba su aikata laifin komai ba a barikin Giwa.

Ta ce an saki wadannan mutane rukuni-rukuni ne, kuma har an mika su ga gwamnatin jihar Borno.

Gambo ta ce a baya-bayan nan ma an saki mutane 28 daga cikin wadanda aka samu ba su da hannu a ayyukan ta’addanci ko kuma cikin kungiyar Boko Haram.

Jihar Borno da ke  arewa maso gabashin Najeriya ta shafe  sama da shekaru 13 tana fama da ayyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram mai ikirarin jihadi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dimbim mutane tare da rabba dubbai da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.