Isa ga babban shafi

Kotu ta umarci gwamnatin Najeriya ta sassauta farashin abinci

Babbar kotun tarayyar Najeriya da ke zamanta a Legas, ta umarci gwamnatin kasar da ta yi gaggawar daidaita farashin kayan abinci da kuma man fetur.Kotun ta ce ta ba wa gwamnatin Najeriya wa’adin kwanaki bakwai da ta aiwatar da umarnin da aka bata.

Wata kasuwar saida kayayyakin abinci a birnin Legas dake kudancin Najeriya.
Wata kasuwar saida kayayyakin abinci a birnin Legas dake kudancin Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa, wanda ya yanke hukuncin, bayan korafin da masu gabatar da kara suka gabatar, karkashin jagorancin babban lauya, Femi Falana.

Falana ya gurfanar da hukumar kayyade farashin kayayyaki ta kasar da kuma babban mai shari’a na tarayya gaban kotun, domin duba sashe na 4 (1) na dokar kayyade farashin kaya da aka yiwa gyaran fuska a shekarar 2004.

Masu gabatar da kara na neman ko wannan hukuma na amfani da wancan sashe wajen kayyade farashin kaya.

A cewar babban lauyan a baya ana sayen shinkafa kan naira 8,000 amma a halin yanzu farashin ya ninka fiye da yanda ake tsammani a kasuwanni, abin da ya jefa al’ummar kasar, musamman masu karamin karfi cikin mummunan yanayi.

Tsadar farashin kaya, ya tilastawa masu shagunan abinci kara farashi, domin samun riba.

Hakan ta sanya alkalin kotun, mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa, umartar gwamnati da tayi gaggawar kayayyade farashin madara, fulawa, sukari, shinkafa da sauran dangogin kayan abinci da kuma farashin man fetur nan da mako guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.