Isa ga babban shafi

Wasu mazauna kauyuka na taimakawa mayakan boko haram - Janar Musa

Najeriya – Hafsan hafsoshin sojin Najeriya, Laftanar Janar Christopher Musa ya zargi wasu al'ummomi dake yankin arewa maso gabashin kasar da taimakawa 'yan ta'addan boko haram a yakin da jami'an tsaro ke fafatawa da su.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Laftanar Janar Christopher Musa
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Laftanar Janar Christopher Musa © Sawaba Radio
Talla

Janar Musa ya bayyana cewar lokacin da yake jagorancin rundunar yaki da mayakan boko haram da ake kira 'Operation Hadin Kai', 'yan ta'addan sun kawo hari, inda sojoji suka hallaka su, amma sai mazauna kauyen suka kwashe makaman wadanda aka kashe, suka yi amfani da su wajen kai wa sojojin hari.

A wata hira da ya yi da tashar TV Trust, Janar Musa ya bukaci shugabannin gargajiya da malaman addini da su fadakar da mabiyan su a kan muhimmancin rayuwa ta gari, musamman ganin yadda matasan yanzu ke rungumar dabi'un da suka ci karo da wadanda aka sani a baya.

Babban hafsan sojin yace abin takaici ne yadda a yau mutane suka fi fifita kudi a maimakon gaskiya da rikon amana.

Hukumomin tsaro sun dade suna zargin bata gari da taimakawa mayakan boko haram a kauyuka wajen basu bayanai da kuma taimaka musu lokacin kai hare haren da suke yi a kai a kai.

Najeriya ta kwashe sama da shekaru 14 tana yaki da mayakan boko haram, tashin hankalin da ya fantsama zuwa cikin kasashen dake makotaka da kasar irin su Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.