Isa ga babban shafi

An yi ruf da ciki kan kudaden da aka warewa 'yan sa kan da ke yakar 'yan ta'adda a Najeriya

A jihar Borno da ke Najeriya, an samu rabuwar kawuna a tsakanin shugabannin kungiyar matasa ‘yan sa-kai da ke taimakawa wajen aikin samar da tsaro a yankin wato Civilian JTF.  

Dakarun na kokari sosai wajen taimakawa jami'an tsaro
Dakarun na kokari sosai wajen taimakawa jami'an tsaro © PremiumTimes
Talla

Rikicin ya kunno kai ne, bayan da aka zargi shugaban kungiyar wadda ke taimaka wa jami’an tsaro domin fada da ayyukan ta’addanci a yankin cewa, ya yi ruf da ciki a kan wasu kadarori cikin har da motoci da aka bai wa Civilian JTF. 

Dakarun na JTF dai na taimaka wa jami'an tsaron, wajen yakar masu tayar da kayar baya, musamman a aarewa maso gabashin Najeriya da ke fama da mayakan Boko Haram da kuma rundunar ISWAP da ta kasance tsagin kungiyar IS ko kuma Al-Qaeda.

Tun bayan bullar kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, aka fara samar da yan sa-kai da ake kira Civilian JTF a jihar Borno.

Shiga alamar sauti, domin sauraron rahoton Bilyaminu Yusuf.

Rundunar ta JTF na taimakawa sojoji sosai wajen yaki da mayakan Boko Haram inda aka ba su makamai tare da biyan su albashi.

A baya gwamnatin Nigeria ta ce za ta soma daukar 'yan sa kai da aka fi sani da civilian JTF aikin soja, domin su taimaka wa sojojin kasar wajen yaki da masu tayar da kayar baya.

Rikicin Boko Haram ya hallaka dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu, musamman a arewa maso gabashin Najeriya da kuma makwabtan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.