Isa ga babban shafi

An kama masu sayar da kunzugun mata a matsayin filo a Sokoto

Jami'an Civil Defence a Najeriya sun kama wasu mutane da ke cusa kunzugun al'adar mata cikin matashin-kai ko kuma filallikan da suke sayar wa jama'a a jihar Sokoto. 

Wani matashin-kai mai dauda.
Wani matashin-kai mai dauda. Shutterstock
Talla

Kwamandan Jami'an Civil Defence na jihar Sokoto, Bello Alkali Argungu ya bayyana cewa, sun kama mutanen tara ne bayan sun samu wasu bayanai na sirri.

Suna amfani da kananan yara da ke tsinto musu sharar. Suna cike matashin-kai da sharar da suke sayar wa kwastamominsu. Filallikan na dauke da mabanbantan tambari na manyan kamfanoni. Inji Argungu.

Wannan dabi'ar ka iya jefa lafiyar al'umma cikin hadari kamar yadda Argungu ya bayyana a lokacin gabatar da mutanen ga manema labarai.

Masu amfani da wadannan filallikan ka iya kamuwa da wata cuta cikin rashin sani, yana mai rokon jama'a da su rika shiga cikin halastattun harkoki.

Ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin kafin daga bisani a mika mutanen da ake zargi ga kotu domin fuskantar hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.