Isa ga babban shafi

Tinubu ya umarci gaggauta kamo masu hannu a kisan jihar Filato

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da harin da ya bayyana mafi muni da aka kai a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na Jihar Filato, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama, inda ya bayar da umarnin a gaggauta kamo wadanda suka aikata kashe-kashen.

Yadda wani hari ya salwantar da rayukan tarin mutane a jihar Filato ta Najeriya.
Yadda wani hari ya salwantar da rayukan tarin mutane a jihar Filato ta Najeriya. AP - APTN
Talla

Shugaban, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya umurci hukumomin tsaron kasar da su gaggauta shiga lungu da sako, tare da kamo masu hannu a lamarin.

Shugaba Tinubu ya kuma ba da umarnin a gaggauta samar da kayan agaji ga wadanda suka tsira daga hare-haren da aka kai da kuma bayar da kulawar da ta dace ga wadanda suka jikkata.

Yayin da yake jajantawa gwamnati da al'ummar jihar Filato, shugaban ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa wadannan jakadun da ya kira na mutuwa, ba za su tsira daga hukumomin kasar ba.

Itama kungiyar Amnesty International ta yi kira ga mahukuntan Najeriya da su binciki duk wani harin da aka kai jihar Filato, tare da tabbatar da hukunta wadanda suka aikata laifin.

Amnesty International ta ce, gazawar hukumomi wajen gurfanar da masu aikata irin wannan danyen aiki a gaban kuliya yana kara ta’azzara lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.