Isa ga babban shafi

Mayakan boko haram sun hallaka masu aikin gawayi 11 a jihar Barno

Najeriya – Wasu da ake zargin mayakan boko haram ne a Najeriya sun hallaka akalla mutane 11 a karamar hukumar Damboa dake Jihar Borno lokacin da suke aikin saran itace da kuma mayar da shi gawayi domin samun abinda za su ci da iyalansu.

Mayakan Boko Haram
Mayakan Boko Haram AFP
Talla

Rahotanni sun ce mayakan sun tare masu yin iccen ne a yammacin jiya litinin a kauyen Damboa Iga dake kusa da Bale, inda suka hallaka wasu daga cikin su.

Wata majiya daga jami’an sakai dake aiki a yankin, tace an samu gawarwakin mutane 6 daga cikin wadanda ke aiki a wurin, bayan an daddatsa sassan jikinsu, kuma har anyi janaizarsu kamar yadda addinin Islama ya tanada, yayin da 5 kuma suka bata.

Wani shaidar gani da ido da ya tsallake rijiya da baya, yace mutanen suna aiki ne a wajen da suke saran itace suna mayar da shi gawaki, lokacin da mayakan haye a kan rakuma suka afka musu, bayan sun musu kawanya.

Mutumin ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar, lokacin da yake gudu, mutanen sun bi shi, amma da yake ya fisu sanin yanayin wurin, sai ya tsere musu.

Mutumin yace daga nan yaje ya shaidawa jama’ar gari, inda suka yi gangami zuwa wurin, amma sai suka tarar da gawarwakin wadannan mutane guda 6 da aka daddatsa su, yayin da ayau talata aka samu karin gawarwaki 5 na mutanen da suka bata.

Rahotanni sun ce sojoji na can suna sintiri a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.