Isa ga babban shafi

Aikin samar da ruwan sha na gwamnati ya bata a jihar Adamawa bayan kammala shi

Najeriya – Ministan kula da ayyukan samar da ruwan sha a Najeriya, Bello Goronyo ya bayyana matukar kaduwarsa da bacewar aikin kwangilar samar da ruwan sha da gwamnatin tarayya ta bayar a jihar Adamawa, inda ya bukaci ‘dan kwangilar da ya je ofishinsa dake Abuja domin yin bayani a kai.

Ministan samar da ruwan sha Bello Goronyo da tawagarsa
Ministan samar da ruwan sha Bello Goronyo da tawagarsa © Daily Trust
Talla

Rahotanni sun ce ministan ya ziyarci jihar Adamawa ne domin gani da ido a kan kwangilar ta naira miliyan 128 da aka baiwa wani kamfanin da ake kira ‘America West African Agro Ltd’ wanda ‘dan kwangilar yace ya kammala, amma kuma sai aka nemi aikin aka rasa.

Rashin ganin aikin duk da ikrarin kammalawar da ‘dan kwangilar ya yi, ya tada hankalin ministan, wanda nan take ya bukaci wanda aka bai wa aikin ya kai kansa Abuja domin yin bayani a kai.

Goronyo yace gwamnatin tarayya a shirye take wajen tabbatar da cewar ana gudanar da ayyukan kwangilar da ta bayar kamar yadda aka amince, yayin da za’a dauki mataki a kan duk wani ‘dan kwangilar da ya saba ka’ida ko kuma ya há’inci jama’a.

Wannan matsalar dai ta kin aiwatar da kwangilolin gwamnati ba sabon abu bane a Najeriya, lura da yadda bincike daban daban da majalisun tarayya ke yi a kan irin wadanna ayyuka kan nuna an fitar da makudan kudade amma kuma babu aikin a kasa.

Yanzu haka hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC na bin diddigin irin wadannan kwangiloli na gwamnatin tarayya da dama da aka fitar da kudade amma kuma ba’a san inda aka kai su ba .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.