INEC ta bayyana Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben Imo
Hukumar zaben Najeriya, INEC ta bayyana Gwamna Hope Uzodinma na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Imo da aka gudanar a jiya Asabar.
Wallafawa ranar:
Abayomi Sunday ,jami’in hukumar zabe ta INEC daga cibiyar tattara sakamakon zaben jihar dake Owerri, ne ya bayyana wanda ya lashe zaben a safiyar yau Lahadi.
Hope Odidika Uzodinma dan takarar APC ya samu kuri’u 540,308 inda ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Samuel Anyanwu, wanda ya samu kuri’u 71,503 yayin da dan takarar jam’iyyar Labour, Athan Achonu, ya zo na uku da kuri’u 64,081.
Hukumar zaben Najeriya ganin cewa Hope Odidika Uzodinma ya cika dukkan ka'idojin a bangaren da ya shafi doka,banda haka ya kuma samu rinjayen kuri'un da suka dace, an ayyana shi a matsayin wanda aka zaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu