Isa ga babban shafi

Kotun Musulunci ta Kano ta zane 'yan daudu saboda rawar badala

Kotun Shari'ar Musulunci da ke zamanta a Hukumar Hisbah ta jihar Kano da ke Najeriya ta yanke wa wasu 'yan daudu hukunci bayan sun yi shigar mata dan yin rawar karya kwankwaso a wajen bikin uban gidansu.

Tambarin shari'ar kotu.
Tambarin shari'ar kotu. © Aminiya
Talla

 

Kotun karkashin jagorancin mai shari'a Mallam Sani Tamim Sani Hausawa ta samu matasan 'yan daudun da laifin ne bayan an karanto musu kunshin tuhumar da ake yi musu, inda nan take suka amsa, sai dai sun roki kotun ta yi musu sassauci.

Mai Shari'ar ya yanke musu hukuncin daurin watanni uku ko zabin biyan tarar naira dubu goma-goma kowannensu  tare da yi musu bulala goma-goma.

Mukaddashin Kwamandan Hukumar Hisbah na jihar Dr. Mujahiddin Aminuddin Abubakar , ya bayyana cewa hukumar ba za ta gajiya ba wajen dakile ayyukan badala domin aikin hukumar shi ne yin hani da aikata mummuna tare da kiran aikata kyakkyawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.