Isa ga babban shafi

Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Emefiele

Hukumar hana zambar kudi da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a Najeriya, ta kama tare da tsare tsohon gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emiefiele.
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emiefiele. © Daily Trust
Talla

Jaridar Punch da ake wallafawa a kasar, ta ce a daren Alhamis ne hukumar ta kama tsohon gwamnan babban bakin kasar, kasa da sa’a guda da ya fito daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya DSS, inda a yanzu yake shalkwatar hukumar EFCC da ke Abuja don gudanar da bincke.

Wata majiya ta tabbatarwa jaridar a safiyar Juma’ar nan cewar, EFCC na gudanar da binciken Emefiele ne game da zargin rashin gudanar da aikinshi yadda yakamata, a lokacin da ya ke gwamnan babban bankin kasar.

Jaridar ta ce ta yi kokarin jin tabakin kakakin hukumar EFCC Dele Oyewale, amma abin yaci tura.

Tun bayan dakatar da Emefiele da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu yayi a watan Yunin daya gabata, hukumar DSS ta kamashi ta kuma tsareshi.

A ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata aka gurfanar da shi a gaban kotu, amma sai dai aka bada belinsa akan naira miliyan 20, kafin daga a soke tuhume-tuhume biyun da ake masa.

Daga bisa an sake tuhumar Emefiele da aikata wasu laifuka 20, wanda ya amince a kulla yarjejeniya ta yadda zai bayar da wani kaso na kudaden da ake tuhumarsa akai.

Daga cikin sharudan yarjejeniyar, akwai yin murabus daga matsayinsa kuma a ranar 22 ga watan Satumba a hukumanci babban bankin na CBN ya tabbatar da murabus dinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.