Isa ga babban shafi

Kotu ta daure mutumin da ya yi yaudarar aure da sunan Buhari

Kotu a Najeriya ta yankewa wani matashin hukuncin daurin watanni 12 a gidan yari, sakamakon kama shi da laifin yaudara da kuma damfarar sirikar sa ta hanyar yi mata alkawarin hada ta aure da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. 

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari AP - Christophe Ena
Talla

Tun farko matashin dan asalin jihar Neja mai suna Gambo Adamu, ya rudi sirikar tasa mai suna Sa’adatu Aliyu, inda ya ce mata tsohon shugaban Muhammadu Buhari ya nuna sha’awar auren ta kuma ya aiko shi don ya shige masa gaba. 

Ba tare da wata-wata ba kuma mai kara Sa’adatu ta amince da shiga fadar Villa, dalili Kenan da ya sa sirikin nata wato mijin ‘yar ta ya rika karbar kudade a hannun ta har Naira miliyan 5, duk a kokarin da ake yi na shirin aure. 

Yayin da ta ke yiwa kotun karin haske Malama Sa’adatu, ta ce sirikin nata ya kai mata naira dubu 100 da huhun goro da kuma soyayyiyar kaza a matsayin sadakin ta da kuma ‘yan kayan makulashe da aka ci lokacin daurin auren ta da shugaba Buhari, abinda ya rage mata yanzu kawai shine ta fara shirin tarewa. 

Sai dai kuma shiru-shiru masoyin nata bai zo daukar ta ba bai kuma aiko anzo daukar ta cikin jerin gwanon motoci da jiniya ba, dalili kenan da ya sa ta tunkari kotu, bayan da ta fara zargin matashin da damfarar ta. 

Baya ga wadannan kudi da matashi Gambo ya karba daga hannun ta ya sanya ta kashe wasu miliyoyin kudi, ta hanyar sanyata kafa kungiya mai zaman kanta da ya ce shugaban Buharin ne ke son bata kwangila da kuma kujerun aikin hajji don ta rawaba ‘yan uwa da abokan arziki, amma shi sirikin nata shi ne zai zama kakakin kungiyar ta yadda kudaden tallafawa kungiyar zasu rika isowa ta hannun sa. 

Da ya ke yanke hukuncin mai shari’a Ibrahim Musa Zango ya yankewa matashin daurin watanni 12 a gidan yari, saboda yaudara da kuma tarar naira dubu 100. 

Haka kuma zai biya mai kara diyyar naira miliyan 2, saboda bata mata lokaci da ya yi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.