Isa ga babban shafi

Najeriya ta fara yunkurin ceto 'yan kasar da aka garkame a Habasha

Majalisar Dattawan Najeriya ta fara bincike a game da makomar wasu ‘yan kasar akalla 250 da ake ci gaba da tsarewa a kasar Habasha, a daidai lokacin da alkaluma ke nuni da cewa akwai wasu daruruwan ‘yan Najeriya da ke daure a wasu kasashe da dama na duniya. 

Akwai dimbin 'yan Najeriya garkame a gidajen yari a Habasha
Akwai dimbin 'yan Najeriya garkame a gidajen yari a Habasha AP - TSVANGIRAYI MUKWAZHI
Talla

Yanzu haka akwai sahihan bayanan da ke tabbatar da cewa akwai ‘yan Najeriya da ke ci gaba da kasancewa a gidajen yarin kasashe da dama a duniya, da suka hada da Afirka ta Kudu, Libya da  kuma Aljeriya, yayin da Majalisar Dattawan Najeriyar ke ci gaba bincike a game da wasu ‘yan kasar da ke daure a gidajen yarin kasar Habasha. 

Farfesa shehu Abdullahi Zuru, masani ne na dokar kasa da kasa, ya bayyana cewa dole ne jakadan Najeriya da ke kasar Habasha ya zage dantse tare da goyon bayan Ministan Harkokin Wajen muddin suna son ceto 'yan kasar da ke garkame a Habashar

Kazalika, farfesa Zuru ya ce idan har aka gaza warware wannan batu a diflomasiyyance, to, Najeriya tana da hurumin gabatar da zance a gaban Majalisar Dinkin Duniya. 

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoto kan wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.