Isa ga babban shafi

Zan tura Atiku kauye ya ci gaba da kiwon awaki - Kashim Shettima

A wani mataki da ke zama murnar nasara a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi wa daya daga cikin wadanda suka gabace shi, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar shagube.

Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima
Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima © kashim shettima facebook
Talla

Atiku, wanda ya yi mataimakin shugaban kasa tsakanin 1999 zuwa 2007, ya fafata da Shugaba Bola Tinubu a zaben ranar 25 ga Fabrairu kuma ya zo na biyu, amma ya kalubalanci sakamakon zaben.

Sanata Kashim Shettima ya ce zai mayar da dan takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar kauyensu ya kuma saya masa dabbobi domin ya yi kiwo.

Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan hukuncin kotun kararrakin zaben shugaban kasa na ranar Laraba da aka tabbatar musu da nasara, inda ya kwashe sama da sa’o’i 12.

Tambayoyin 'Yan jaridu

Da yake amsa tambayar wani dan jirada kan makomar Atiku a siyasance, masamman ritaya da ya taba cewa zai tura tsohon shugaban a lokacin yakin neman zabe.

Kashim Shettima ya ce “A yanzu ana cikin yanayi ne na mulki, an wuce batun zabe, kuma Atiku Abubakar dattijon kasa ne da yake girmamawa"

To sai dai duk mastayinsa na Kanuri, wanda akwau barkwancin tsakaninsu da Fulani yanada damar tsokanarsa yadda ya ga damaya.

“Don haka ba za mu mayar da Atiku Dubai ko Morocco ba, a maimakon haka zamu mayar da shi Fombina, in saya masa awaki da kaji domin ya yi kiwo''.

Tsohon gwamnan na Barno yaci gaba da cewa ''A gaskiya, Atiku dattijon ne, kuma Najeriya na bukatar irinsu".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.