Isa ga babban shafi

INEC na da damar fayyace tsarin fitar da sakamakon zabe - Kotu

Kotun da ke sauraren kararkin zaben Najeriya ta ce baya cikin dokokin hukumar zaben kasar cewa dole sai hukumar zaben mai zaman kanta INEC ta rika bayyana sakamakon zabe a fili.

Shugaban hukumar INEC farfesa Mahmud Yakubu kenan, lokacin da yake karbar sakamakon jihohi na zaben shugabancin kasar da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Shugaban hukumar INEC farfesa Mahmud Yakubu kenan, lokacin da yake karbar sakamakon jihohi na zaben shugabancin kasar da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023. AP - Ben Curtis
Talla

Yayin yanke hukuncin, mai shari’a Haruna Tsammani ya ce dokokin da suka samar da INEC sun bata damar zabar yadda  take sha’awar ayyana sakamakon zabe, ko dai ta barshi ga jama’a su rika gani tun daga matakin mazaba ko kuma ta bari sai an gama tattarawa gaba daya.

Ko da ya ke karanto sashe na 52 da 65 na dokokin da suka kafa hukumar INEC sun ce babu damar wata hukuma ko kuma Kotu su yiwa INEC katsalandan game da yadda zata tattara da kuma ayyana sakamakon zabe.

Alkalin na wadannan bayanai ne a lokacin da yake jingine karar jam’iyyar Labour kan cewa INEC ta yi kumbiya-kumbiya wajen ayyana sakamakon a shafukan yanar gizo tun daga matakin mazaba.

Har yanzu dai kotun bata gai ga yanke hukuncin karshe kan kararrakin da aka shigar ba, sai dai ana sanya ran a yau din ne zata kammalla ta kuma fitar da hukunci na karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.