Isa ga babban shafi

An tsaurara matakan tsaro a Abujan Najeriya gabanin hukuncin sakamakon zaben shugabancin kasar

An tsaurara matakan tsaro a Abuja, babban birnin Najeriya, yayin da ya rage kwana guda kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke hukunci kan makomar zaben shugabancin kasar da aka yi a watan Fabrairun 2023, wanda Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour ke kalubalantar nasarar da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC ya samu.

Atiku Abubakar da kuma Peter Obi su ke kan gaba wajen kalubalantar sakamakon zaben, inda su ke neman a soke zaben, saboda zargin an tafka magudi.
Atiku Abubakar da kuma Peter Obi su ke kan gaba wajen kalubalantar sakamakon zaben, inda su ke neman a soke zaben, saboda zargin an tafka magudi. © Daily Trust
Talla

Daraktan ma’aikatar tsaron kasar, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya gargadi masu shirin tayar da tarzoma bayan hukuncin kotu, da su kuka da kansu, domin kuwa jami’an tsaro za su dauki mataki mai tsauri a kan su.

A ranar Litinin ne, kotun sauraron kararrakin zaben ta sanar da cewa za ta zartas da hukuncin karshe kan kararrakin da ke gabanta wadanda ke kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu.

A ranar daya ga watan Maris ne,shugaban hukumar zaben Najeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ayyana Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban Najeriya, bayan da jam’iyyarsa ta samu rinjayen kuri’un da aka kada.

A zaben na 2023, tsohon gwamnan jihar Legas, ya samu sama da kuri’u miliyan takwas, wanda hakan ya bashi nasara kan abokin karawarsa Atiku Abubakar da ya samu kuri’u kusan miliyan bakwai, sai Peter Obi da ya samu sama da miliyan shida na kuri’un da aka kada masa.

Sai dai Atiku Abubakar da kuma Peter Obi su ne ‘yan takarar da ke kan gaba wajen kalubalantar sakamakon zaben, inda suke neman a soke zaben, saboda zargin an tafka magudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.