Isa ga babban shafi

Tinubu na shirin ganawa da Biden kan makomar demokradiyya a Afrika

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya roki takwaransa na Amurka Joe Biden da ya tallafa wa kasashen Afrika daga barazanar masu yi wa tsarin demokradiyya karan-tsaye a ciki da wajen nahiyar, da nufin samar da ingantacciyar rayuwa ga jama'a.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. © AP/Gbemiga Olamikan
Talla

Tinubu wanda ke wannan kira yayin karbar bakoncin mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka a nahiyar Afrika Molly Phee a Abuja, ya bayyana cewa tabbas nahiyar na bukatar taimakon Amurka wajen tabbatuwar demokradiyya a kasashensu.

Ms Phee wadda ke shaida wa Tinubu bukatar shugaba Joe Biden ta ganawa da shi, yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke tafe a birnin New York.

Bayanai na nuni da cewa yayin ganawar ta Tinubu wanda ke matsayin shugaban kungiyar ECOWAS za su taba batutuwan da suka shafi makomar mulkin demokradiyya a kasashe mambobin kungiyar musamman wadanda suka fuskanci juyin mulkin soji a baya-bayan nan.

Mashawarcin shugaba Tinubu na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa baya ga Tinubu Joe Biden zai kuma gana da shugabannin kasashen Afrika da za su halarci taron.

Shugaba Tinubu ya ce, akwai bukatar samar da sabbin tsare-tsaren amfani da kudaden tallafin raya kasashe da Amurka ke bai wa Afrika a wani yunkuri na tabbatar da dorewar demokradiyya a kasashe masu tasowa da ke fuskantar tarnaki.

A cewar shugaban dole ne a yi hakan da himma kamar yadda cibiyoyin suka tsare-tsare don tallafa wa Turai bayan kammala yakin duniya na biyu, ya kara da cewa hakan zai taimakawa kasashen Afrika wajen magance matsalolinsu.

Shugaban na Najeriya ya ce kamfanoni masu zaman kansu za su yi jagoranci tun da mun riga mun samar da farfajiya.

Kuma yakamata gwamantin Amurka ta kirkiri masana’antu da kuma zuba jari a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.