Hukumomin Chadi sun karbi tubabbun mayakan boko haram 46
Rundunar Hadin kai ta kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi dake yaki da mayakan boko haram MNJTF ta sanar da mika tubabbun mayakan 46 ga hukumomin Chadi.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da kakakin rundunar Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya rabawa manema labarai tace kwamandan sashe na 2 na rundunar ta MNJTF, wato Manjo Janar Djouma Youssouf Mahamat Itno ne ya shugabanci mika wadannan tubabbun mayaka 46 ga jami’an gwamnatin Chadin a karshen wannan mako.
Kanar Abdullahi yace an yi bikin mika su ne a Bagasoli, kuma ya samu halartar ministan kula da ayyukan jama’a Abdoulaye Mbodou Mbami wanda ya karbe su a madadin gwamnati.
Wannan na daga cikin fadada ayyukan da rundunar ke yi tare da gwamnatin Chadi na ganin an baiwa mayakan kwarin gwuiwar aje makaman su domin rungumar zaman lafiya.
Yayin da yake tsokaci a wajen bikin, Janar Itno ya bukaci sauran mayakan dake daji da su bi sahun wadannan 46 wajen aje makaman su, yayin da ya jinjinawa shugabannin al’umma akan rawar da suka taka na fadakar da jama’a illar daukar makamai.
Bikin ya samu halartar muhimman mutane, cikin su harda Gwamnan Yankin Lac, Janar Djibrine Ratou da Kantoman Yankin Kaya, Hassane Abderamane da kuma sarakunan gargajiya.
Kanar Abdullahi ya bayyana bikin a matsayin wata gagarumar ci gaba a yunkurin da rundunar ke yin a kawar da ayyukan ta’addanci a yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu