Isa ga babban shafi

Musulman Lagos na zanga-zanga saboda hana su kujerun kwamishina

Shugabannin al'ummar Musulmi a jihar Lagos da ke Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a harabar Majalisar Dokokin Jihar domin nuna rashin amincewarsu da matakin da gwamnan jihar ya dauka na nada Kiristoci 39 a matsayin kwamishinoni, yayin da aka nada Musulmai 8, abin da suka ce sam ba za su yarda da shi ba.

Musulman Lagos a harabar Majalisar Dokokin Jihar
Musulman Lagos a harabar Majalisar Dokokin Jihar © Daily Trust
Talla

Tun da fari, al'ummar Musulmin sun fusata da jerin sunayen da aka fitar na kwamishinonin, inda suka ce, gwamna Babajide Sanwo-Olu bai yi musu adalci ba, yayin da suka bukace shi da ya sake nazari musamman ganin yadda ke da dimbin yawa a jihar.

Sai dai gwamnatin jihar ta yi watsi da bukatar Musulman a yayin da Majalisar Dokokin Jihar ta fara zamanta a ranar Litinin domin tantance kwamishinonin.

A wannan Larabar, shugabannin al'ummar Musulman karkashin jagorancin Farfesa Tajudeen Gbadamosi sun yi dafifi a haraabar Majalisar Dokokin Jihar domin nuna adawarsu da abin da suka bayyana  a matsayin nuna wa Musulman wariya.

Musulman na rike da wasu alluna masu dauke da mabanbantan sakwanni da ke cewa, " Musulmai sun ce ba su amince da nuna wariya a hukumance ba"  " Abin da muke bukata shi ne adalci"  " A dakata da wannan tantancewar a yanzu" " Muna bukatar adalci" da dai sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.