Isa ga babban shafi

Tsadar gidajen haya ta karu da kashi 40 a manyan biranen Najeriya

Wani rahoton bincike ya nuna cewa an samu karin tsadar kudin gidajen haya da kashi 40 cikin 100 a manyan biranen Najeriya, daga farko zuwa tsakiyar shekarar 2023 da muke ciki.

Wasu gidajen haya a Najeriya
Wasu gidajen haya a Najeriya © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Masanan sun danganta tsadar kudin gidajen hayar da matsalolin karuwar farashin kayayyaki da kuma karin kudaden ruwan da ake dorawa kan basukan da bankuna ke bayar wa daga kashi 16.5 zuwa kashi 18.75.

Kasuwar hada-hadar gidaje a Najeriya ta kara yi wa masu karamin karfi nisa a baya bayan nan ne, musamman a biranen Legas, Abuja, Enugu, Fatakwal da kuma Kano.

Masu ruwa da tsaki kan hada-hadar gine-gine sun matsalar na da nasaba da rashin daidaita farashin saye da sayarwa da kuma bayar da hayar gidaje daga bangaren mahukunta, abinda ya sa masu kumbar susa ke cin karensu babu babbaka, sai kuma tsadar farashin kayayyakin gine-gine.

Wani bincike ya nuna cewar a garin Legas, gidaje masu dakuna biyu da dakin dafa abinci da bandaki sai ‘yar farfajiya, a baya ana bayar da hayarsa akan naira dubu 400 ga misali a yankin Ikeja, a yanzu farashin ya karu  zuwa naira dubu 600 a duk shekara, yayin da a yankin Lekki farashin ya tashi daga tsakanin naira dubu  800 da naira miliyan da rabi a duk shekara, zuwa tsakanin naira miliyan 1 da rabi ko miliyan 3 a shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.