Isa ga babban shafi

Jam'iyar APC ta nada Kyari a matsayin mukaddashin shugabanta

Jam’iyar APC ta nada mataimakin shugabanta da ke kulada yankin Arewacin Najeriya, Sanata Abubakar Kyari a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyar na kasa, biyo bayan murabus din da shugabanta Sanata Abdullahi Adamu ya yi.

Abubakar Kyari, mugaddashin shugaban Jam'iyar APC mai mulki a Najeriya.
Abubakar Kyari, mugaddashin shugaban Jam'iyar APC mai mulki a Najeriya. © APC twitter
Talla

A cewar dokar jam’iyar, a duk lokacin da shugaba da ke kai ya yi murabus daga matsayinsa, mataimakinsa da ke kula da yankin da ya fito ne zai maye matsayinsa.

A yanzu haka Kyari na jagorantar taron kwamitin gudanarwar jam’iyar a sakatariyarta da ke babban birnin kasar Abuja, cikin tsauraran matakan tsaro.

Daga cikin wadanda suka halarci taron, akwai mataimakin shugaban jam’iyar da ke kulada yankin Kudancin kasar Emma Enukwu da mataimakin shugaban jam’iyar mai kulada shiyar Arewa maso yammaci Salihu Lukman da takwarorinsa na shiyar Arewa maso Gabas Salihu Mustapha da na Tsakiya Muazu Bawa da na Kudu maso yammaci Issacs Kekemeke da na Kudu maso Gabas Ejoroma Arodiogu sai kuma mataimakin sakataren jam’iyar na kasa Barista Festus Fuanter.

Kyari ya kasance dan siyasa daga jahar Borno, inda ya rike mukamin kwamishina daga shekarar 2003 zuwa 2005 da kuma shekarar 2007 zuwa 2011.

A shekarar 2015, an zabe shi sanatan da ke wakiltar Arewacin Borno a karkashin inuwar jam’iyar APC, kuma aka sake zabensa a shekarar 2019, matsayin da yak e rike har zuwa lokacin da aka nadashi matsayin mataimakin shugaban jam’iyar da ke kulada yankin Arewcin Najeriya a shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.