Isa ga babban shafi

APC ta zabi shugabannin Majalisar Tarayyar Najeriya ta 10

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta zabi Sanata Godswill Akpabio a matsayin wanda take son ya zama shugaban Majalisar Dattawan kasar ta 10, inda Barau Jibrin zai kasance mataimakinsa.

Shugaban Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya,  Abdullahi Adamu.
Shugaban Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Adamu. © Kola Sulaimon/AFP
Talla

Kazalika jam'iyyar ta APC ta sanar da Hon. Abbas Tajudeen matsayin kakakin Majalisar Wakilai, yayin da Ben Kalu zai zama mataimakinsa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen rantsar da zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a cikin watan Fabairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.