Isa ga babban shafi
LABARIN AMINIYA:

’Yan Majalisa sun bukaci karin albashi bayan cire tallafin mai

Mambobin Majalisar Wakilai sun bukaci a kara musu albashi da kudaden alawus-alawus bayan cire tallafin man da suka ce ya sanya farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabi.

Kakakin Majalisar wakilai Tajudeen Abbas
Kakakin Majalisar wakilai Tajudeen Abbas © aminiya
Talla

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa bukatar ta biyo bayan tattaunawar da majalisar ta yi ranar 11 ga watan Yuli, yayin wani zaman jagororinta.

Rahotanni sun ce korafe-korafen da mambobin majalisar suka yi ne ya sa dole aka yi zaman domin a kwantar musu da hankula.

Sun dai kalubalanci Kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas, kan dalilin da ya sa aka bata lokaci ba a biya su albashi da alawus-alawus dinsu ba, ta yadda sai da wasu daga cikinsu suka koma cin bashi.

To sai dai daya daga cikin ’yan majalisar da yake cikin wajen da aka tattauna, amma ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba shi da hurumin yn magana a kan batun, ya ce babu kamshin gaskiya a labarin.

Ya ce abin da kawai suka shaida wa Kakakin shi ne kudaden da suke samu ba za su isa su biya bukatunsu na yau da kullum ba, dalili ke nan da suka bukaci a yi musu karin.

Dan majalisar ya ce sun aike da bukatar ce la’akari da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki da kuma tsadar kayayyaki.

Sai dai ya ce Kakakin bai yi musu wani alkawarin cewa za a yi karin ba, saboda za a yi hakan ne kawai a cikin kasafin kudi. (NAN)

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.