Isa ga babban shafi

Najeriya: ‘Yan Bindiga Sun Kashe masu hakar ma’adanai 3 a jihar Filato

Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai uku aka harbe a jihar Filato dake Najeriya, bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai wani wurin hakar ma’adinai da ke kusa da Tanjol dake cikin al’ummar Jol a karamar hukumar Riyom ta jihar.

'Yan bindiga na ci gaba da addaba sassan daban-daban na Najeriya.
'Yan bindiga na ci gaba da addaba sassan daban-daban na Najeriya. © dailytrust
Talla

Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Matasan Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust faruwar lamarin, inda ya ce sauran masu hakar ma’adinai da manoma da ke kusa da su sun tsare daga yankin.

A cewar Tengwong, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar jumma’a, daidai lokacin mazauna yankin ke gudanar da harkokinsa, inda ya kara da cewa wasu mutane biyu sun jikkata.

Sakataren yada labaran, wanda ya bayyana harin a matsayin wanda ke kara yawaita a yankin, ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar karkara.

Ya ce duk da tura jami’an ‘yan sandan tafi da gidanka a yankin, ana ci gaba da kashe-kashen ba tare da tsayawa ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, bai amsa kiran jaridar ba,  amma wani babban jami’in ‘yan sanda da bai so a ambaci sunansa ya tabbatar da faruwar harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.