Isa ga babban shafi

Tinubu na ganawar sirri da sarki Sunusi a Abuja

Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi na ganawa da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ziyara a fadar sa ta Aso Rock Villa, da ke Abuja.

Karon farko kenan da shugaban ya gana da basaraken.
Karon farko kenan da shugaban ya gana da basaraken. © dailytrust
Talla

Sanusi ya isa Villa ne sa'o'i bayan shugaban kasar ya kaddamar da majalisar tattalin arzikin kasa. Taron ya samu halartar gwamnoni da dama da kuma manyan mataimakan shugaban kasa.

Alkiblar tattalin arzikin wannan gwamnati dai ya yi dai-dai da tunanin Sanusi, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya.

Basaraken, wanda ya kasance masanin tattalin arziki ya kasance mai rajin kawo karshen tallafin man fetur, manufar da Tinubu ya aiwatar ranar rantsuwar kama aiki.

Wannan shi ne karo na farko da Tinubu da Sanusi suka gana a Aso Rock.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.