Isa ga babban shafi
Kano-Najeriya

Addinin Musulunci bai koyar da bara ba- Sarkin Kano

Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi na II ya ja hankalin mabarata a fadin Najeriya da su koma rokon gwamnati maimakon rokon daidaikun jama’a.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi na II.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi na II. Reuters
Talla

Muhammadu Sanusi wanda ya jima yana nesanta bara da koyarwar addinin Islama kamar yadda wasu ke ikirari, ya ce idan har ya kama dole sai almajiri ya yi bara to babu wanda ya fi cancanta da su roka face gwamnati wadda ita ke da wani kaso na nauyinsu akanta.

Sarkin na Kano, jihar da ke da yawan mabarata matalauta da kuma marasa ilmi, ya ja hanklai kan illolin da ke tattare da dabi’ar aikewa da yara kanana makarantun allo da sunan neman Ilimin addini.

A cewar Mai martaba Sarki Sanusi, duk da kasancewar Ilimin Addini da na zamani wajibi kan kowanne yaro amma kamata ya yi ayi amfani da makarantun gab da gida musamman ga kananan yara ko kuma idan har ya kasance tilas aikewa da yaran makarantu allo to a hadasu da dukkanin kayakin bukata maimakon abarsu suna bara.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito Muhammadu Sanusi na wannan kira ne yayin wani taron Alarammomin Qur’ani da ya gudana a jihar Jigawa da ke da nufin tsaftace harkar karatun allo ko kuma almajirci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.