Isa ga babban shafi

An fara cinkoson sayen fetur a Lagos sakamakon kalaman Tinubu

An fara dogayen layuka a gidajen sayar da man fetur da ke birnin Lagos na Najeriya jim kadan da sanarwar da shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu ya yi ta janye kudin tallafin man fetur.

Sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. © Temilade Adelaja / Reuters
Talla

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, direbobin motoci sun yi cincirindo a gidajen mai na NNPC da ke Ikeja, inda suke rige-rigen sayen man.

Jaridar ta rawaito cewa, da dama daga cikin gidajen man fetur masu zaman kansu ba sa sayar da man ya zuwa lokacin da Daily Trust ta fitar da rahoton.

A yayin gabatar da jawabinsa na shan rantsuwar kama aiki a yau Litinin, shugaba Tinubu ya bayyana cewa, mawadata ne kadai ke amfana da kudin tallafin man fetur din a maimakon talakawa.

Tinubu ya ce, gwamnatinsa za ta karkatar da kudin tallafin zuwa ga bangarorin ilimi da lafiya da samar da ayyuka da gina kayayyakin more rayuwa da za su amfani miliyoyin al’umma.

Kazalika shugaban ya ce, zai nazarci korafe-korafe game da dimbin kudaden haraji don ganin an habbaka tattalin arzikin kasar tare da janyo masu zuba jari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.