Isa ga babban shafi

Buhari ya yi wa magajinsa rakiya wasu wurare na fadar shugaban kasa

Yayin da ya rage kwanaki uku a rantsar da zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, shugaba mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya zagaya da shi lungu da sako na fadar shugabancin kasar, gabanin karbar ragamar mulkin kasar.

Buhari tare da Tinubu
Buhari tare da Tinubu © Presidency/Sallau
Talla
Lokacin da shugabannin suka fara zzagayawa fadar ta Villa.
Lokacin da shugabannin suka fara zzagayawa fadar ta Villa. © Presidency/Sallau

Wannan na zuwa ne kwana guda, bayan mataimakin shugaban kasar mai barin gado, farfesa Yemi Osinbajo, ya yi makamanciyar wannan rakiya ga Kashim Shettima, wato mataimakin zababben shugaban kasar.

Shugaban Najeriya Buhari, tare da magajinsa Bola Tinubu.
Shugaban Najeriya Buhari, tare da magajinsa Bola Tinubu. © Presidency/Sallau

Tuni dai shugaban kasar mai barin gado da mataimakinsa, suka fice daga gidajen da suke zaune a ciki a fadar Villa.

Bola Ahmed Tinubu, yayin da yake musabaha da shugaba Buhari a ofishinsa da ke Villa.
Bola Ahmed Tinubu, yayin da yake musabaha da shugaba Buhari a ofishinsa da ke Villa. © Presidency/Sallau

Haka zalika, dukkanin mukarraban shugaba Buharin, sun yi nisa da fara kwashe kayayyakinsu, yayin da ssuke bankwana da fadar ta Villa.

Wani sashe da ke cikin fadar Villa kenan.
Wani sashe da ke cikin fadar Villa kenan. © Presidency/Sallau

A ranar 29 ga watan Mayun 2023, zabababben shugaban kasar, zai karbi rantsuwar karbar ragamar jagorancin Najeriya, tare da mataimakinsa Kashim Shettima, wato tsohon gwamnan jihar Borno.

Sashen da shugaban kasa ke gudanar da zaman tattaunawa da ministocinsa.
Sashen da shugaban kasa ke gudanar da zaman tattaunawa da ministocinsa. © Presidency/Sallau

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.