Isa ga babban shafi

'Yan daba sun kai hari kan cibiyar tattara sakamakon gwamnan Adamawa

‘Yan daba dauke da muggan makamai sun kai hari kan cibiyar da hukumar INEC ke tattara sakamakon zaben kujerar gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar Adamawa da ke birnin Yola.

Jami'an zabe a garin Yola na jihar Adamawa.
Jami'an zabe a garin Yola na jihar Adamawa. REUTERS - Nyancho NwaNri
Talla

Wakilinmu Ahmad Alhassan ya shaida mana cewar tun da tsakar daren jiya Lahadi, maharan suka yi wa cibiyar tattara sakamakon zaben na gwamna kawanya tare da hana shiga ko fita daga cikinta, sai dai  daga bisani hadin gwiwar jami’an tsaron ‘yan sanda da sojoji sun kawo karshen tashin hankalin.

Wakilin namu ya shaida mana cewar an kammala tattara sakamakon zaben gwamnan a kananan hukumomi 20 daga cikin 21 da ke fadin jihar ta Adamawa.

Sai dai rashin tabbatar da alkaluman kuri’un da aka kada a karamar hukumar Fufore inda ‘yan daba suka kwace sakamakon, ya sanya hukumar zabe jinkirta shelar dan takarar da yayi nasara har zuwa tsakar yau Litinin.

Tuni kuma jami’an tsaro suk sake kintsa wa wajen shirn ko ta kwana domin tabbatar da da tsaro.

Takara dai ta zafi ne a tsakanin Aishatu Ahmad Binani ta jam’iyyar APC da ke fatan kafa tarihin zama gwamna mace ta farko a Najeriya, sai kuma Ahmadu Finitiri na jam’iyyar PDP, wadanda za a iya cewar kusan kan-kan-kan ake tafiya  tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.