Isa ga babban shafi

Hukumomin Italiya sun cafke 'yar Najeriyar da take tilasta wa mata karuwanci

‘Yan sandan Italiya sun bayyana cewa, Joy Jeff, wata ‘yar Najeriya da ake nema ruwa a jallo tun a shekarar 2010 an tasa keyar ta daga Abuja zuwa birnin Rome inda aka yanke mata hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari bisa samunta da laifin tilasta wa wasu mata yin karuwanci.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumomi na duniya ke koka wa kan yadda ake take hakkin mata
Wannan na zuwa ne yayin da hukumomi na duniya ke koka wa kan yadda ake take hakkin mata The Guardian
Talla

Joy Jeff, mai shekaru 48, ta kasance daya daga cikin mata kalilan da ke cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo a Italiya, in ji ‘yan sanda a cikin wata sanarwa, inda suka bayyana ta a matsayin fitacciyar mace a kungiyar mafiya ta Najeriya.

Yarjejeniyar da Najeriya da Italiya suka sanya wa hannu a shekarar 2020 ne suka taimaka wajen mika matar.

Sanarwar ta ce an kama ta ne a Najeriya a ranar 4 ga watan Yuni, 2022, bisa sammacin kasa da kasa da Italiya ta bayar.

Masu bincike na Italiya a birnin Ancona da ke gabashin kasar sun ce Joy Jeff ta taka rawa wajen safarar mata zuwa Italiya da Spain da kuma Netherlands, inda aka tilasta musu yin karuwanci ta hanyar cin zarafi da barazana.

Bidiyon da 'yan sandan Italiya suka fitar ya nuna yadda aka dauko Joy Jeff daga Abuja babban birnin Najeriya zuwa filin jirgin saman Ciampino da ke Rome inda 'yan sanda suka dauke ta a keken guragu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.