Isa ga babban shafi

Ranar mata: Za'a yi shekaru 300 kafin cimma daidaito tsakanin maza da mata-Guterres

A daidai lokacin da mata ke gudanar da bikin su a wannan rana, haka nan an shirya tattaki a titunan manyan biranen kasashe a fadin duniya, don nuna rashin amincewa da yadda ake ci gaba da take hakkinsu.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. © Hadi Mizban / AP
Talla

Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi kashedin cewa ana samun koma baya a game da hakkokin mata, inda ya sadakar cewa za’a shafe wasu Karin shekaru 300 kafin a cimma daidaito tsakanin mata da maza.

A jajibirin wannan rana, kungiyar Tarayyar Turai ta kakaba takunkumai a kan wasu daidaikun mutane da kasashe da ta ce suna da nasaba da cin zarafin mata.

Daga cikin wadanda aka sanya wa takunkumai har da ministan ilimi mai zurfi na gwamnatin Taliban a Afghanistan, Neda Mohammad Nadeem sakamakon haramta wa mata ilimin jami’a a kasar.

Wannan takunkumi ya shafi jami’ai daga kasashen, Iran da Rasha da Sudan ta Kudu da Myanmar da kuma Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.