Isa ga babban shafi

Mu muka lashe zaben Najeriya - Peter Obi

‘Dan takarar zaben shugaban kasar Jam’iyyar Leba a Najeriya Peter Obi ya sanar da cewar zasu je kotu domin kalubalantar sakamakon zaben da ya nuna cewar Bola Ahmed Tinubu ne ya samu nasara. 

Peter Obi kenan, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ke kada kuri'arsa a Anambra. (2023/02/25)
Peter Obi kenan, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ke kada kuri'arsa a Anambra. (2023/02/25) AP - Mosa'ab Elshamy
Talla

Obi ya shaidawa manema labarai cewar zasu bi duk matakan shari’ar da suka dace ta hanyar lumana domin kwato hakkinsu saboda suna da shaidun dake nuna cewar su suka lashe zaben, kuma zasu nunawa ‘yan Najeriya. 

Alkaluman da hukumar zabe ta gabatar ya bayyana cewar Obi ne ya zo na 3 da kuri’u miliyan 6 da dubu 101 da dari 553, yayin da Bola Ahmed Tinubu ya zo na farko da kuri’u miliyan 8 da dubu 794 da dari 726, yayin da Atiku Abubakar ya zo na biyu da kuri’u miliyan 6 da dubu 984 da dari 520. 

‘Dan takarar Jam’iyyar Labour ya bayyana zaben a matsayin mafi takaddama a tarihin Najeriya saboda yadda aka haramtawa jama’ar kasar abinda suka zaba. 

Zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu yayi kira da abokan takararsa da su hada hannu da shi wajen aikin gina kasa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.