Isa ga babban shafi

An bukaci Amurka kada ta sayar da makamai ga Najeriya kan zub da cikin matan Boko Haram

Wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka da suke cikin kwamitin kula da harkokin kasashen ketare, sun yi kira ga shugaba Joe Biden da ya soke kwangilar saida wa Najeriya makamai, wadanda darajarsu ta kai kusan dala biliyan 1, a bisa zargin sojojin Najeriya da cin zarafin matan da suka shiga hannun kungiyar Boko Haram.

Wasu daga cikin 'yan matan sakandaren Chibok da suka kubuta daga karkashin mayakan Boko Haram, yayin da suka isa wata cibiyar lura da su a birnin Abuja. 30 ga watan Mayu, 2017.
Wasu daga cikin 'yan matan sakandaren Chibok da suka kubuta daga karkashin mayakan Boko Haram, yayin da suka isa wata cibiyar lura da su a birnin Abuja. 30 ga watan Mayu, 2017. Sunday AGHAEZE / PGDBA & HND Mass Communication / AFP
Talla

Bukatar ‘yan majalisar da ke cikin wani  karamin kwamiti  mai kula da nahiyar Afirka, ta biyo bayan rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters, kan zargin rundunar sojin Najeriya da tilasta wa dubban mata zubar da juna biyun da suka samu daga mayakan Boko Haram. 

Sara Jacobs ta jam’iyyyar Democrats da Chris Smith na Republican, sun kuma bukaci gwamnatin Amurka ta sake nazari kan talllafi da kuma wasu yarjeniyoyin hadin gwiwar da take aiwatarwa a Najeriya, sai  kuma udanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa sojin Najeriya wajen haddasa hasarar rayukan fararen hula da kuma cin zarafin dan Adam a sakamakon tallafin makaman da suke samu  daga Amurkan. 

A watan Afrilun da ya gabata, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta amince da sayar da makamai ga Najeriya, gami da bata wasu nau’ikan na tallafin soja, taimakon da shi ne mafi girma da kasar Amurkan ta taba baiwa Najeriyar. 

A baya bayan nan 'yan majalisar dokokin Amurkan suka bayyana cewar ma'aikatan jin kai sun bayar da rahoton jami'an tsaron Najeriyar ba su da cikakkiyar fahimta akan kiyaye dokokin jin kai, zalika sun gaza wajen inganta hulda tsakaninsu da fararen hula. 

Amurka dai ta  dade tana taimakawa Najeriya a fannin tsaro ciki har da horas da sojojinta a bisa tsarin dokokin kasa da kasa, sai  dai  wasu na ganin ya zuwa yanzu taimakon bai yi wani tasiri ba cikin shekaru 14, wajen kawo karshen mayakan Boko Haram, kungiyar da aka samu tsagin ISWAP daga cikinta a yankin arewa maso gabashin kasar, kuma akwai rahotannin cewa masu tayar da kayar bayan sun kwace tarin makamai daga hannun jami’an tsaro a yankin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.