Isa ga babban shafi

Na sayi makaman Dala biliyan 1 don yaki da Boko Haram - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce lokacin da ya karbi ragamar mulkin kasar a shekarar 2015, mayakan boko haram na rike da kashi biyu bisa 3 na kananan hukumomin da ke jihar Borno da rabin kananan hukumomin da ke jihar Yobe da kuma wasu yankunan kananan hukumomin jihar Adamawa. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Bashir Ahmad
Talla

Buhari ya shaida wa taron tsaron da ke gudana a Mauritania cewar, ya kashe kudin da ya zarta Dala biliyan guda wajen sayen makaman da aka yi amfani da su wajen sake karbo wadannan yankuna daga ‘yan ta’addan daga Amurka da wasu kawayen Najeriya. 

Shugaban wanda ya jinjina wa sojojin kasar tare da abokan aikinsu na kasashen Chadi da Nijar da Kamaru da kuma Jamhuriyar Benin da ke yaki a karkashin rundunar hadin gwuiwa, ya ce sun bada gudunmawa sosai wajen ‘yantar da wadannan yankuna. 

Buhari ya ce duk da matsalolin kudaden da kasar ke fuskanta, sun ci gaba da ware kaso mai tsoka na kasafin kudin Najeriya wajen bunkasa bangaren soji domin tinkarar kalubalen dake gabansu. 

Shugaban ya ce wasu daga cikin wadannan kudade ya dace a yi amfani da su ne wajen bunkasa bangaren ilimi da kul ada lafiyar jama’a da samar da kayan more rayuwa, amma kuma rashin zaman lafiya ba zai bada damar cin gajiyar wadannan abubuwa ba. 

Buhari ya ce duk da yake suna samun nasarar yaki da ‘yan ta’addan, Najeriya a matsayinta na kasa da kuma wani bangare na yankin Afirka ta Yamma na fuskantar kalubalen rashin zaman lafiyar da ake samu a kasashen Libya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da wasu yankunan kasashen Sahel da ma yakin da ke gudana a Ukraine, saboda yadda makamai ke kwarara daga wadannan wurare zuwa yankin. 

Shugaban ya ce ya zama wajibi shugabannin Afirka su goyi bayan shirin tabbatar da zaman lafiya da kuma siyasar dake gudana a kasashe irinsu Libya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da wasu yankunan Sahel domin dakile yaduwar tashe tashen hankula da aikata laifuffuka da kuma dakile yaduwar sojojin haya na ciki da wajen Afirka. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.