Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta bukaci Kotun Koli ta janye umurnin ta kan tsoffin Naira

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bukaci Kotun Kolin kasar ta janye umarnin da ta yi a ranar Laraba da ke yin watsi da dokar daina amfani da tsaffin takardun kudi na Naira, hukuncin da ke nuna dakatar da wa’adin Juma’an nan 10 ga watan Fabarairu da babban bankin kasar CBN ya kayyadewa al’umma na ganin sun kammala mika tsaffin takardun kudinsu ga banki don karbar sababbi. 

Shugaba Buhari tare da Godwin Emefiele.
Shugaba Buhari tare da Godwin Emefiele. © Sunday Aghaeze>2022/ Arise News
Talla

Wata wasika da lauyoyin ma’aikatar shari’ar Najeriyar Mahmud Magaji da Tijanni Gazali suka mika ga kotun kolin ta ruwaito Ministan shari’ar na cewa babu wasu kwararan hujjoji da zai sanya kotun har ta yanke hukunci kan karar da ke neman dakatar da wa’adin. 

Ganawa da Buhari

Sa’a'o’i kalilan bayan wata ganawar shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan babban bankin na CBN da kuma Abubakar Malami a fadar Aso Rock ne wannan kalamai kan kalubalantar hukuncin kotun ya fito ga jama’a. 

Yayin ganawar dai Shugaban ya tattaunawa da Emifiele da kuma Malami ne kan halin da ake ciki game da sauya fasalin kudin kasar. 

Gwamnonin APC

Tun farko dai gwamnaonin jam’iyyar APC 3 da suka kunshi na jihar Kogi Yahya Bello da na Kaduna Malam Nasir El Rufa’i da kuma na Zamfara Bello Matawalle ne suka shigar da karar gaban kotun koli da ke neman dakatar da bankin na CBN daga daina amfani da takardar kudin a daga ranar Juma’a 10 ga watan Fabarairu. 

Sai dai Abubakar Malami ya bayyana cewa wadanda suka shigar da korafi kan lamarin basu da wasu kwararn hujjoji kan dalilin yin hakan, wanda ke nuna bukatar da ke akwai ga kotun kan ta janye hukuncin na ta. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.