Malami ya maida martani kan bukatar biyan Igboho diyya
Gwamnatin Najeriya na shirin daukaka kara kan hukuncin wata babbar kotu a jihar Oyo da ke a birnin Ibadan, da ta umarci gwamnati da ministan shari’a su biya diyyar naira biliyan 20 ga mai rajin kare muradun kabilar Yarbawa Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho, a matsayin diyyar barnar da jami'an tsaron farin kaya na DSS suka yi masa yayin wani sumame da suka kai gidansa.
Wallafawa ranar:
Dan rajin dake naman ballewar yankin kudu maso yamamcin Najeriya na hannun hukumomin Benin a halin da ake ciki tun bayan tserewarsa lokacin da jami'an na DSS suka dira a gidansa.
To sai dai yayin da yake martani kan matakin cikin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja Ministan Shari’a Abubakar Malami ya sanar da cewa za a daukaka kara kan hukuncin.
Tun bayan tserewar Sunday Igboho lauyoyinsa suka maka hukumar ta DSS da ministan shari'a na Najeriya a gaban kuliya, inda a madadinsa, suke neman a biya shi kudade saboda take hakkinsa na dan kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu