Isa ga babban shafi

Cutar Mashako ta Diphtheria ta kashe mutane 38 a jihohin Najeriya 4

Alkaluman wadanda cutar mashako ta Diptheria ta kashe a jihohin Najeriya 4 ya kai mutum 38 yayinda wasu 123 suka harbu da cutar mai matukar hadari.

Zuwa yanzu cutar ya bazu a jihohin Najeriya 4.
Zuwa yanzu cutar ya bazu a jihohin Najeriya 4. AFP PHOTO/Mauricio Ferretti
Talla

Hukumar da ke yaki da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta ce jihar Kano ke da alkaluma masu yawa na wadanda suka harbu da cutar dama wadanda cutar ta kashe inda ta ke da kumullar mutum 100 da suka harbu kana wasu 32 suka mutu.

Jihar Yobe ke biye da Kano da jumullar mutum 17 da suka harbu da cutar kana wasu 3 suka mutu sai Lagos mai mutane 5 ciki har da 3 da cutar ta kashe yayinda jihar Osun ta sanar da harbuwar mutum guda.

Babban daraktan hukumar ta NCDC Ifedayo Adetifa yayin jawabinta gaban wakilcin manyan jami’an hukumar lafiya ta kasar ta bayyana irin hadarin da ke tattare da cutar ta Diphtheria dama bukatar daukar matakan gaggawa don kawar da barazanar ta da dakile yaduwarta zuwa sauran sassan kasar.

NCDC wadda tuni ta sanya cutar a sahun cutuka masu hadari da ke yaduwa cikin sauri tsakanin jama’a ta roki hukumomin lafiya a matakin jihohi da su mike tsaye don dakile yaduwar cutar ta Diphtheria.

A cewar hukumar hanya daya ta magance harbuwa da cutar ga kananan yara shi ne tabbatar da cewa sun samu rigakafin wajibi da ake yi tun daga haihuwa zuwa shekaru 5.

Cutar wadda ke sahun cutukan da kwayoyin bakteriya ke haddasawa na tokare makogwaro da hanci ko ta kai ga illa ga fata, yayinda wasu daga cikin alamominta ke kasancewa zubar majina ba kakkautawa zazzabi ko ciwon makogwaro baya ga tari da sauyawar launin ido zuwa ja sai kumburin wuya wanda ke kaiwa ga gaza lumfashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.