Isa ga babban shafi

NCDC na zaman shirin ko ta kwana bayan bullar cutar Diptheria a jihohin Kano da Lagos

Hukumar yaki da cututtuka a Najeriya NCDC ta ce jami’an ta na ci gaba da sanya ido akan halin da ake ciki a Jihohin Lagos da Kano, sakamakon barkewar cutar mashako ko kuma diptheria wadda ta kashe mutane kusan 30 kawo yanzu. 

Zuwa yanzu cutar ta kashe mutane 30.
Zuwa yanzu cutar ta kashe mutane 30. AP - Sunday Alamba
Talla

Shugaban hukumar NCDC Ifedayo Adetifa ya kuma ce suna sanya ido akan jihohin Osun da Yobe inda ake fargabar samun wadanda suka harbu da ita. 

Alkaluman ma’aikatar lafiyar Kano sun ce akalla mutane 25 suka mutu daga cikin mutane 58 da suka harbu da cutar, yayin da wasu guda 6 ke kwance a asibiti. 

NCDC ta bayyana cutar mashakon a matsayin wadda sinadarin bakteria ke haifarwa wajen kama hanci ko makogoro, yayin da wani lokaci ta kan shafi fatar jikin Bil Adama. 

Hukumar ta bayyana alamomin cutar da suka hada da zazzabi da kwararar majina daga hanci da ciwo a makogoro da tari da jan ido da kuma kumburar wuya. 

NCDC ta bukaci iyaye da su kai yaransu domin yi musu allurar rigakafin kamuwa da cutar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.