Isa ga babban shafi

Sai kun nuna sakamakon zaben mazaba kafin na ba ku mukami - Atiku

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya shaida wa magoya bayansa cewar, sai sun nuna sakamakon zaben mazabar da suka fito kafin samun mukaman gwamnati ko kuma kwangila idan ya samu nasara a zabe mai zuwa. 

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kenan Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kenan Atiku Abubakar © premium times
Talla

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce yin haka ne kawai zai sanya ‘ya'yan jam’iyyar jajircewa wajen ganin kowa ya koma mazabarsa domin yi wa PDP aiki a zaben watan gobe. 

Atiku ya shaida wa magoya bayansa a Jihar Ogun cewar tafiyar da suke da ‘dan takaran shugaban kasa ko gwamna ko kuma sanata ba dama ba ce na samun mukami idan jam’iyyar ta samu nasara, saboda haka dole sai kowa ya koma mazabarsa domin tabbatar da cewar jam’iyyarsu ta samu nasara a wurin. 

Dan takarar ya ce wannan matsayi nasa, ba wai ya tsaya kawai ga masu neman mukamin gwamnati ba ne, har da masu neman kwangilar yi wa gwamnati aiki a matakan gwamnatin tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi. 

Atiku ya ce da zaran ya zama shugaban kasa, abin da zai mayar da hankali a kai kenan daga duk wanda ya tinkare shi domin samun mukamin gwamnati ko kuma kwangila. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.