Isa ga babban shafi

Maganar rashin lafiyata shirme ne kawai - Tinubu

Dan takarar shugabancin Najeriiya karkashin jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana zancen rashin lafiyarsa da aka yi ta yayatawa a matsayin tsohon labari da kuma shirme.

Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu © daily trust
Talla

Tinubu ya fadi haka ne a zantawar da ya yi da kafar Freedom Radio a yayin gudanar da ibadar Umara a Saudiya, yana mai cewa, yanzun nan ya kammala sassarfa tsakanin dutsinan Safa da Marwa har sau bakwai, wanda mutun mara koshin lafiya ba zai iya ba a cewarsa.

Masu sukar Tinubu dai na ci gaba da cewa, ba zai iya jagorancin Najeriya ba saboda dalilai na rashin cikakkiyar lafiya.

Sai dai a cewar dan takarar na APC,  yanzu yanzu ya kammala gudanar da aikin Umara tare da kewaye dakin Ka’aba sau bakwai da kuma kai-kawo tsakanin Safa da Marwa, yayin da ya diga ayar tambaya kan ko mara lafiya zai iya irin wannan aikin?

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage ‘yan makwanni a gudanar da babban zaben shugabancin Najeriya, inda Tinubu zai fafata da manyan ‘yan takara irinsu Atiku Abubakar da Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Peter Obi da dai sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.