Isa ga babban shafi

Obasanjo ya goyi bayan Obi a zaben 2023

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya fito karara ya goyi bayan dan takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar Labor, wato Peter Obi, gabanin zaben 2023 da zai guda a cikin watan Fabairu.

Peter Obi da kuma Olusegun Obansanjo
Peter Obi da kuma Olusegun Obansanjo © Vanguard
Talla

Obasanjo ya bayyana haka ne a sakonsa na sabuwar shekara mai taken “ Rokona ga daukacin ‘yan Najeriya musamman matasa”.

Tsohon shugaban kasar ya ce, babu tsarkakakke tsakanin ‘yan takarar shugabancin Najeriyaa, amma idan aka duba fannin ilimi da sanin-ya-kamata  da kuma abin da za su iya yi, to babau kamar Obi.

Obasanjo ya bayyana Obi a matsayin mabiyin-sahunsa kuma a cewarsa, tsohon gwamnan na jihar Anambra na kan gaba a jerin ‘yan takarar a zaben 2023.

Obi dai zai fafata da manyan 'yan takarar da suka hada da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki, da Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da kuma Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.