Isa ga babban shafi

Tinubu ya sha alwashin tattaunawa da IPOB idan ya hau mulkin Najeriya

Dan takaran shugaban kasar Jam’iyyar APC a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu yace idan ya lase zabe mai zuwa zai tattauna da kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra da kuma irin ta dake sashen kudu maso gabashin kasar. 

Dan takarar neman kujerar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu.
Dan takarar neman kujerar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu. © Bola Tinubu
Talla

Tinubu ya ce ta hanyar tattaunawarce kawai za a saurari korafinsu da kuma zummar nazari akai ta hanyar warwaresu domin tabbatar da zaman lafiya a Najeriya. 

Dan takaran ya shaidawa magoya bayansa da ke jihar Imo cewar Najeriya na bukatar zaman lafiya, saboda haka ya zama wajibi a gare shi da ya zauna da irin wadannan kungiyoyi domin ji daga wakilansu kai tsaye. 

Tsohon gwamnan Lagos ya kula alkawarin zuba jari mai karfi a bangaren ilimi domin yaki da talaucin da ya addabi jama’a da kuma tabbatar da kawo sauyi ta hanyar da yara za su samu ilimi. 

Dangane da gudumawar da yankin kudu maso gabashin Najeriya ke bayarwa ta bangaren tattalin arziki kuwa, Tinubu ya ce zai mayar da yankin kamar Taiwan da ke nahiyar Asia wadda ta yi fice a wannan bangaren. 

Fafutukar ballewar yankin kudu maso gabas daga Najeriya da kungiyar IPOB ke jagoranci ya haifar da tashe tashen hankula da kuma kungiyoyin da suka dauki makamai wadanda ke kai hare hare suna kasha jama’a. 

Magoya bayan kungiyar sun kuma tilastawa jama’ar yankin daina harkokin yau da kullum kowacce litinin, matakin da ya taimaka sosai wajen karya tattalin arziki sakamakon rufe kasuwannin da ake yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.