Isa ga babban shafi

Shin na yi kama da mara lafiya ? - Tinubu

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya diga ayar tambaya kan ko ya yi kama da mara lafiya, inda ya hakikance cewa, shi yana da koshin lafiyar jagorantar kasar.

Asiwaju  Bola Ahmed Tinubu 
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu  STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

A yayin gabatar da jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta APC a birnin Kano, Tinubu ya caccaki masu fadin cewa, ba shi da lafiya.

Ba wai zan yi tseren tsawon yadi 100 ko kuma 500 ba ne, Ina neman kujerar shugaban kasa ne. Ba kuma ina takara ba ne a gasar damben zamani. Idan na fita, sai su ce ba ni da lafiya. Yanzu ina tsaye a gabanku, shin na yi kama da mara lafiya ?”  Inji Tinubu 

Kazalika dan takarar ya kuma yi alkawarin cewa, ba zai bai wa magoya bayansa kunya ba muddin aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan Najeriya ke cewa, Tinubu bai cancaci tsayawa takarar shugabancin kasar ba a zaben 2023 bisa la'akari da halin da yake ciki na rashin lafiya da rashin karsashi, inda a baya-bayan nan ya yi balaguro zuwa kasar waje domin duba lafiyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.