Isa ga babban shafi

Kotu a Najeriya ta umarci INEC ta ci gaba da rijistar katin zabe

Babbar kotun tarayya da ke Abujan Najeriya, ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar (INEC) da ta gaggauta ci gaba da gudanar da rijistar masu kada kuri’a har zuwa kwanaki 90 kafin zaben 2023.

Wasu daga cikin masu zabe a Najeriya
Wasu daga cikin masu zabe a Najeriya STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Mai shari’a Inyang Ekwo, a hukuncin, ya kuma umurci INEC da ta tabbatar da cewa ba a hana wa ‘yan Najeriya da suka cancanta damar samun katin zabe a zabe mai zuwa ba.

Mai shari’a Ekwo ya ce alhakin da tsarin mulki ya rataya a wuyan alkalan zaben ne su bada gudun mowa sosai ga shirin gudanar da zaben kamar yadda dokokin Najeriya suka tanada.

A farkon sammacin da suka gabatar a gaban kotun, masu shigar da kara sun ce INEC ba za ta iya dakatar da rijistar katin zabe ba, sabanin yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Sun bukaci kotun da ta umarci hukumar zaben ta ci gaba da rijistar ‘yan kasar, kamar yadda dokar kasar ta tanada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.