Isa ga babban shafi

Ba zan duba lafiyata a wata kasa ba muddin aka zabe ni a 2023 - Kwankwaso

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin cewa, zai yi amfani da dukkanin ikonsa don hana kansa zuwa kasashen ketare da nufin neman magani muddin aka zabe shi a 2023.

Rabi'u Musa Kwankwaso
Rabi'u Musa Kwankwaso © Premiumtimes
Talla

Kwankwaso ya bayyana haka a yayin da yake jawabi a wani zaman taro kan zaben 2023 da gidan talabijin na Channels ya shirya a ranar Lahadi.

Kalamansa na zuwa ne a yayin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya dawo daga balaguron da ya yi zuwa birnin London domin duba lafiyarsa kamar yadda ya saba akai-akai.

A ranar 31 ga watan Oktoba ne, shugaba Buhari ya fice daga kasar.

Kwankwaso ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta inganta bangaren kiwon lafiya tare da samar da kayayyakin aiki a asibitoci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.